Gwamna Inuwa ya ƙaddamar da rabon abinci karo na 17 a Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya kaddamar da rabon kayan abinci a karo na 17 ga marasa galihu da nakasassu kimani dubu ɗari biyu da sha huɗu da ɗari biyar.

Za a yi rabon kayan abincin ne a rumfunar zaɓe guda dubu 2,218 da ke mazaɓu 114 a faɗin jihar.

Gwamnan ya ce, ya fara ba da irin wannan tallafin ne tun a zangonsa na farko, inda ya raba sau 15.

Ya ce a yanzu bayan dawowarsa wannan shi ne karo na biyu kuma jimilla na 17 idan an haɗa da wanda ya yi a baya.

Gwamnan ya kira al’ummar jihar Gombe da su ci gaba da taimaka wa juna da ɗan abin da suke samu.

Ya kuma roƙi da su ci gaba da yi wa Jihar Gombe da Nijeriya addu’ar dorewar zaman lafiya.

A jawabinsa, shugaban kwamitin rabon kayan abincin wanda shi ne Mataimakin Gwamnan jihar, Dokta Manassah Daniel Jatau da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar, Abubakar Inuwa Kari ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar tana sane da irin matsalolin tattalin arziƙin da al’ummar jihar ke fuskanta musamman na ƙarancin abinci.

Ya ce, abin ya sa aka kafa ƙananan kwamitocin masu ruwa da tsaki a matakin gundumomi da ƙananan hukumomi shi ne don tabbatar da rabon kayan abincin cikin tsanaki.

By Editor