Harin Mairuwa: Gwamnan Raɗɗa zai tallafa wa iyalan waɗanda abin ya shafa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa na jihar Katsina ya yi Allah wadai da harin da ‘yan bindiga suka kai a garin Mairuwa da ke Ƙaramar Hukumar Faskari a jihar, inda ya bayyana hakan a matsayin rashin tausayi.

Harin wanda ya afku a yammacin ranar Asabar ɗin da ta gabata a lokacin sallar magariba a watan Ramadan da muke ciki, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu biyu.

Gwamna Raɗɗa, ta bakin sakataren gwamnatin jihar Barista Abdullahi Garba Faskari ya yi Allah wadai da harin tare da jajantawa.

Ya kuma yi alqawarin tallafa wa iyalan waɗanda suka rasu, sannan ya buƙaci mazauna yankin da su yi addu’ar Allah ya dawo da matar da ‘yarsa da aka sace.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya dawo da shi yankin lafiya.

Alhaji Lado Mairuwa, babban manomi ne kuma ɗan kasuwa wanda ya bayar da gudunmuwa ta ɓangarori da dama ya bayar da gudunmuwa ta vangarori da dama.

Marigayi Lado ya bar mata huɗu da ‘ya’ya 26, yayin da makwabcinsa, Sani Abdullahi wanda shi ma aka kashe a lokacin da yake ƙoƙarin taimakon marigayin ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 20.

Domin ƙara ta’azzara matsalolin iyalai, ‘yan fashin sun sace matar marigayin, Hajiya Rabi, da ɗiyarsa mai shekaru 14, Maryam. Har yanzu ba a san inda suke ba.

A yayin ziyarar ta’aziyyar ɗan marigayin Umar Abdulhamid mai shekaru 18, wanda lamarin ya faru a gaban idonsa ya ce ‘yan bindigar sun harbe mahaifin nasa ne bayan ya bijirewa yunqurinsu na ɗauke shi.

Ya kuma tabbatar da cewa, wani makwabcinsu Sani Abdullahi da ya zo taimako shi ma ‘yan bindigar sun harbe shi har lahira.

Yayin da suke yabawa da damuwar gwamnan da kuma ƙoƙarin gwamnatinsa na magance matsalolin tsaro, mazauna garin Mairuwa sun roƙi gwamnatin tarayya da ta dauki ƙwaƙƙwaran mataki.

Sun kuma yi kira da a ƙara tsaurara matakan tsaro a jihar Katsina da makwabta kamar Zamfara da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga.