Gwamna Inuwa ya kai labari a Kotun Ƙoli

Daga BASHIR ISAH

Kotun Ƙoli a ranar Juma’a ta tabbatar wa Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, nasarar da ya samu a zaben 2023.

Kotun ta yanke hukuncin haka ne bayan da ta yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar PDP a zaben na ran 18 ga Maris, 2023, Mohammed Barde ya daukaka inda yake kalubalantar nasarar da Inuwa ya samu.

Barde ya daukaka kara ne kan cewa zaben da ya bai wa inuwa nasara cike yake sa badakalar sayen kuri’u.

Sai dai baki daya shari’o’in da aka yi kan zaben a kotuna matakai uku, sun tabbatar da Inuwa a matsayin zababben Gwamnan Gombe.