Gwamna Lalong ya cancanci muƙamin Sakataren Gwamnatin Tarayya a gwamnatin Tinubu – NCAF

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jagororin jam’iyyar APC a ƙarƙashin Ƙungiyar North Central APC Forum, sun yi kira ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu, da ya zaɓi Simon Lalong a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya a gwamnatinsa.

A cewar ƙungiyar, ba Simon Lalong muƙamin na SGF zai kuma tabbatar da cewa anyi adalci a cikin gwamnati mai zuwa ta yadda kowane ɓangare zai yi na’am ya san ana damawa da shi.

Da yake jawabi a madadin ƙungiyar a birnin Jos bayan sun gudanar da taron gaggawa, shugaban ƙungiyar Alhaji Saleh Mandung Zazzaga, yace Lalong ya wahaltawa APC, Arewacin Nijeriya, a matsayin sa na shugaban gwamnonin Arewacin Nijeriya, jihar Plateau da zaman Tinubu shugaban ƙasa.

A kalamansa, “Gwamna Simon Lalong yayi sadaukarwa sosai ga APC, Arewacin Nijeriya, ƙasa gabaɗaya. Mutum ne mai son zaman lafiya wanda ya samu nasarori da dama kuma shugaba ne wanda baya nuna wariya. Wani abin burgewa dangane da shi shine rawar da ya taka a zaɓen shugaban ƙasa na APC.”

“Ƙungiyar mu da sauran ƙungiyoyi da wasu manyan mutane mun yi kiran da a bashi takarar shugaban ƙasa daga yankin Arewa ta Tsakiya saboda gudunmawar da yankin ya bayar, Amma ba muyi nasara ba, sai muka koma neman a bashi mataimakin shugaban ƙasa tun da an amince a miƙa mulki zuwa yankin Kudu”

“Saboda haka ƙoƙarin da Lalong yayi ya sanya yakamata a bashi matsayin SGF. Ba wai kawai ya dace da kujerar bane, amma ya cancanta kuma zai kawo ƙwarewarsa wajen shugabanci domin ciyar da ƙasar nan gaba,” in ji ƙungiyar.