Masari ya bayyana dalilin korar wasu jami’ansa

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa ya ƙagara 29 ga watan mayu ta zo, saboda a cewarsa ya matsu ya sauka daga kan kujerar mulkin gwamnan jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da gidan talabijin na TVC cikin shirin ‘Politics On Sunday’ wanda Manhaja ta bibiya.

Masari ya ce a matsayinsa na gwamnan jihar ya rasa ‘yancinsa na zuwa inda yake so ba tare da jami’an tsaro ba, ya rasa ‘yancin tuƙa mota da wasu abubuwa da yake son yi da kansa, don haka ne ya ƙagara ya bar kujerar gwamnan ko ya samu damar kasancewa da iyalansa gami da ziyarar ‘yan uwan da abokai.

Daga nan ya bayyana dalilin da yasa ya kori wasu daga cikin jami’an gwamnatinsa lokacin da ake tsaka da gudanar da manyan zaɓuka a ƙasar nan.

“Mun kori wasu daga cikin jami’an gwamnati saboda sun ci amanarmu.

“Sun ci amanar amincewar da muka yi masu don haka babu dalilin da zai sa su ci gaba da riƙe muƙaman siyasa da aka ba su, saboda su ba ma’aikatan gwamnati ba ne,” inji shi.

A cewarsa, bai ga dalilin da zai sa mutum ya ciji hannun da ke ba shi abinci ba.

Gwamna Masari ya ce kodayake shi ba zai bar siyasa baki ɗaya ba, sai dai ya ce ba zai kuma sake tsayawa takarar wata kujera ba.

Da aka tambayi gwamnan ko mene ne dalilin da ya sa jam’iyyar APC ta faɗi zaɓen Shugaban Ƙasa a Jihohin Katsina,Kano da kuma Lagos?

Ya ce, manufar Babban Bankin Nijeriya na sauya kuɗi shi ne sanadi, saboda a cewarsa Gwamnan Babban Bankin ya ɓata ran masu zaɓe a ƙasar nan.