Gwamna Lawal ya ƙaddamar da gina sabuwar tashar motoci ta zamani a Gusau

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamna Dauda Lawal ya sake tabbatar da ƙudurin gwamnatinsa na samar da ayyukan yi ga al’ummar da ke dogaro da harkokin tasha. A ranar Litinin, gwamnan ya ƙaddamar da gina sabuwqr tashar motoci ta zamani a babban titin Sokoto-Zaria da ke Gusau, babban birnin jihar kamar yadda Mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris ya fitar. An ba kamfanin Fieldmark Construction LTD kwangilar aikin, wanda zai ƙunshi wuraren ajiye motoci masu faɗi, wuraren hutawa ga direbobi, tsare-tsaren tsaro na zamani, da tsarin tikiti mai sauƙi domin inganta gudanar da ayyuka.

Da yake ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana wannan aiki a matsayin muhimmin ɓangare na ƙudirin gwamnatinsa na inganta gine-ginen birni a Gusau. Ya ce: “Wannan shiri zai inganta tsaro, ƙara samun kuɗaɗen shiga da kuma bai wa birninmu damar yin gogayya da sauran birane a faɗin kasar” .

Gwamnan ya ce, tashar za ta ƙunshi kayayyakin more rayuwa na zamani kamar layin tashi, ofishin ‘yan sanda, asibiti, wurin kashe gobara, masallaci, ginin gudanarwa, ofishin ƙungiyar direbobi, ɗakunan wanka na jama’a, otal, filin lodin kaya, shaguna, terminal na matafiya, wurin zubar da shara, rumbun ajiya, ɗakin gyaran mota da wurin wanke motoci. A cewarsa, aikin zai ɗauki ma’aikatan da ba su ƙware ba da kuma ma’aikatan da suka ƙware, sannan zai zama cibiya ta kasuwanci bayan kammala shi, wanda zai amfani ‘yan kasuwa da sauran masu sana’o’i .

Gwamnan ya jaddada cewa kayan more rayuwa irin su tituna da ya fara gina wa tun bayan hawa mulki yana daga cikin hanyoyin da za su inganta harkokin kasuwanci da kuma samar da ci gaban tattalin arziki. Ya kuma yi addu’ar Allah ya albarkaci wannan aiki da ya zama alheri ga al’ummar jihar Zamfara .

By ukarofi