Daga USMAN KAROFI
Shugaban ƙaramar hukumar Igbo Etiti da ke Jihar Enugu, Eric Odo, ya amince da naɗin wani mashawarci na musamman kan har harkokin noma, musamman akan yaji da yalo.
A cewar naɗin da aka yi, an naɗa Nwodo Everestus Ugonna domin ya kasance mai ba da shawara kan harkar noma, tare da taimakawa a fannin yalo da yaji. Haka kuma, an naɗa Ezeugwu Frederick Ogbonna a matsayin mai ba da shawara kan harkar noma, musamman kan harkokin doya.
A cikin takardar naɗin su wacce aka sanya hannu ranar 1 ga Nuwamba, an umurci Nwodo da Ezeugwu su je ofishin shugaban ƙaramar hukuma da ke Ogbede don samun ƙarin bayani da tsarin aikin su. Takardar ta bayyana cewa, “Ina mai farin cikin sanar da kai cewa shugaban ƙaramar hukumar Igbo Etiti ya amince da naɗin ka a matsayin babban mashawarci na musamman kan harkokin noma musamman doya da yaji.”
Haka zalika, Ugonna samu takardar naɗin ta shi wacce ta bayyana cewa: “Muna farin cikin sanar da kai cewa shugaban ƙaramar hukumar Igbo Etiti ya amince da naɗin ka a matsayin babban mashawarci na musamman kan harkokin noma musamman kan yalo da yaji.”
An kuma bayyana cewa wannan aiki ba yana cikin tsarin aikin gwamnati na dindindin ba, sai dai kawai wani aikin wucin gadi da ke ƙarƙashin ikon shugaban ƙaramar hukumar Igbo Etiti.
