Tinubu ya yi kwaskwarima ga tawagar yaɗa labaransa

Spread the love

Daga BELLO A BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kwaskwarima wa tawagar da ke yaɗa labaran ofishinsa don inganta harkokin ɓangaren a gwamnatinsa.

Ya ce daga yanzu, Bayo Onanuga da Sunday Dare da kuma Daniel Bwala za su riƙa aiki tare a matsayin masu magana da yawun gwamnatin.

Cikin wata takarda da Onanuga ya fitar a ranar Talata, ya ce Tinubu ya yanke hakan ne don tabbatar da isar da saƙon gwamanti game da tsare-tsare, matakai da sauran aikace-aikace akan lokaci da inganci.

Shugaba Tinubu ya yi nuni da muhimmanci yin aiki hannu-da-hannu a lamuran da suka shafi ofishin yaɗa labarai.

Sunday Dare, wanda da shi ne Mai bada Shawara na Musamman kan Labarai da Wayar da kan Al’umma, yanzu an naɗa shi a matsayin Mai bada Shawara kan Harkokin Labarai da Sadarwa ga Al’umma.

Haka kuma, Daniel Bwala wanda a makon da ya gabata aka naɗa shi Mai bada Shawara kan Labarai da Sadarwa ga Al’umma, yanzu kuma ya samu matsayin Mai bada Shawara na Musamman kan Labaran da suka shafi Tsare-tsare yayin da kuma Bayo Onanuga ya cigaba da riƙe muƙaminsa na Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai.

By Babaji