Daga USMAN KAROFI
Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) da Birtaniya (UK) sun ƙara ƙaƙaba wa Iran sabbin takunkumi saboda zargin da ake mata na goyon bayan Rasha a yaƙin da take yi da Ukraine. Sabbin matakan sun shafi manyan tashoshin jiragen ruwa na Iran, kamfanonin jigila da kuma wasu cibiyoyin gwamnati da ake zargi da taimaka wa Rasha wajen samun jiragen yaƙi marasa matuki da makamai masu linzami. Wannan takunkumi ya hana Iran sayarwa ko samar da kayayyakin da ake amfani da su wajen ƙera makamai ga Rasha.
Sabbin matakan da EU ta ɗauka sun haɗa da dakatar da duk wani nau’i na kasuwanci da tashoshin jiragen ruwa da ke ƙarƙashin ikon mutane ko ƙungiyoyin da aka ƙaƙaba wa takunkumi. Wannan ya shafi tashoshin Amirabad da Anzali, waɗanda ake zargin su na taimaka wa Rasha wajen jigilar kayan yaƙi. Sanarwar da EU ta fitar ta ce, duk da haka, ana iya tallafa wa jiragen ruwa da ke cikin hatsari a yankin domin ceto su, bisa doka ta tsaron teku.
Bugu da ƙari, EU ta ƙaƙaba takunkumi ga kamfanin jigilar kaya na gwamnatin Iran, IRISL da daraktansa Mohammad Reza Khiabani, tare da wasu kamfanonin jigila na Rasha guda uku da ake zargi da ɗaukar makamai ta hanyar tekun Caspian zuwa Rasha. Wannan ya biyo bayan takunkumin da aka ɗauka tun da farko kan jami’an gwamnatin Iran da kuma wasu kamfanonin jiragen sama da ake zargi da taimaka wa Rasha wajen yaƙin.
Ita ma Birtaniya ta ɗauki matakin kulle kadarorin IRISL da Iran Air, kamfanin jirgin saman ƙasar Iran, wanda ake zargin ya na jigilar makamai masu linzami zuwa Rasha. Haka zalika, Birtaniya ta hana jirgin ruwa na Rasha mai suna Port Olya-3 shiga kowane tashar jiragen ruwa na ƙasar. Iran ta musanta dukkan zargin cewa tana jigilar makamai ko jiragen yaƙi zuwa Moscow don yaƙin Ukraine, inda Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce wannan zargi ba shi da tushe ko makama.
