Daga BASHIR ISAH
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sha alwashin gwamnatinsa za ta maido da martabar ilimi a jihar.
Ya bada wannan tabbacin ne a wajen taron ƙaddamar da aikin gyaran makarantun da suka lalace da kuma gina sabbi jihar.
Sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce, Gwamnatin Jihar na bai wa ɓangaren ilimin jihar fifiko ne domin cika alƙawarin da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe.
Sanarwar ta ƙara da cewa, fara aiwatar da wannan ƙudiri ya yi daidai da manufar ayyana Dokar ta Ɓaci a fannin ilimi jihar.
Haka nan, ta ce aikin gyare-gyaren ya haɗa da gina sabbin azuzuwa, gyara tsaffin azuzuwa, katange makarantu, samar da kujerun zama da sauransu.
Bugu da ƙari, sanarwar ta ce za a miƙa kwangilar ayyukan ne ga fitattun ‘yan kwangila kuma ‘yan asalin jihar.
Aikin zai shafi gyara makarantun da suka lalace a tsakanin ƙananan hukumomi 14 a faɗin jihar haɗi da gina sabbin makarantun tsangaya a tsakanin shiyyoyin siyasa guda ukun da jihar ke da su, Anka, Ƙaura Namoda da Gusau.
“Domin aiwatar da waɗannan ayyukan, gwamnati ta ware kuɗi Naira biliyan 4,346,450,209.19,” in ji sanarwar.
