Kotu ta bada belin Emefiele kan N300m

Daga BASHIR ISAH

Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a yankin Maitama a Abuja, ta bada belin tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Kotu ta bada belin nasa ne kan kuɗi Naira miliyan 300.

Yayin zaman shari’a da kotun ta yi a ranar Laraba, Mai Shari’a Hamza Muazu ya buƙaci Emefiele da ya gabatar da shaidu guda biyu, kuma tilas shaidun ya zamana sun mallaki kadarori a yankin Maitama.

Kodayake Emefiele bai halarci zaman kotun ba sakamakon yana tsare a gidan yarin Kuje tun a makon jiya.

Kimanin makonni biyu da suka gabata wata Babbar Kotu a Abuja ta bada odar a saki Emefiele biyo bayan ƙarar take ‘yancin da ya shigar a kan Gwamnatin Tarayya.

Yanzu dai kotun ta ɗage ci gaba da sauraren shari’ar ya zuwa ranar 28 ga Nuwamba, 2023.