Rigima ta ɓarke tsakanin matar jarumi Mista Ibu da ‘yarsa kan kuɗin tallafi da ya samu

Spread the love

Daga AISHA ASAS

A daidai lokacin da shahararren jarumi a masana’antar fim ta Kudu, wato Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da Mista Ibu ke kwance gadon jinya tare da alhinin iftila’in da ya saukar masa, its kuwa maiɗakinsa mai suna Stella Maris, da kuma ‘yarsa ta riqo Jasmine Okafor, suka fara nuna wa juna yatsa danganen da kuɗaɗen da abokanen sana’arsa da masoyansa na faɗin duniya suka yi tururuwar tura masa, sa’ilin da aka nemi taimakon jama’a don sama masa lafiya.

Kamar yadda sanannen shafi a kafar sada zumunta ta Instagram, Gistlover, ya wallafa hoton firar ‘yar ta Mista Ibu da ƙawarta da take labarta mata abinda matar mahaifin nata ke yi, wanda hakan kawai zai tabbatar da varkewar faɗa a tsakanin su.

Firar ba ta qare ba, har sai da ta bayyana dalilin rikicin, wanda ba komai ba ne face ‘yan kuɗaɗen da aka tara wa jarumin a asusun neman taimako da suka fitar a ‘yan watannin baya.

Shafin ya bayyana cewa, ‘yar ta jarumin Jasmine Okafor, na zargin matar mahaifinta da yunƙurin rub-da-ciki da ‘yan kuɗaɗen da aka tara wa mahaifinta, da ƙudurin wadata kanta da ababen mure rayuwa kamar yadda ta saba, har ta ƙara da cewa, yanzu haka tana kan zancen siyan sabuwar waya ta zamani da ta fito kwanan nan ta kamfanin Apple, wato iPhone 15 da kuma sababbin motocin hawa.

Ba iya nan ta tsaya ba, shafin ya kuma bayyana cewa, matar ta jarumi Mista Ibu, ta yi amfani da asusun ajiyarta ta wawuri kimanin Naira miliyan ɗaya daga cikin kuɗaɗen tallafin.

Wannan labarin ya taɓa zukatan mutane da dama, musamman ma masoyan jarumin, inda suka shiga ambaliyar martani daidai da ra’ayoyinsu, sai dai da yawa sun tsayu a vangaren matar tasa.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka yi martani akwai Omalicha Nenye, wadda ta ke ganin furucin ‘yar a matsayin abinda bai dace ba, kuma ta bayyana goyon bayanta ga matar inda ta ce, ” matar Mista Ibu na da haƙƙi da damar juya asusun mijin nata.”

Ita kuwa wata mai suna Edna cewa ta yi, “shiga tsakanin ma’aurata ba abu ne mai kyau ba. Jasmine, kina zancen matarsa ne fa, duk abinda ta so yi a dukiyar mijinta haƙƙinta ne, kuma ba wanda ya isa ya ce mata don me sai ‘yan’uwanshi.”

Oriaku Eternal ta rubuta, “magana ta ƙarshe dai ita ɗin dai matarsa ce, kuma ta haifa masa ‘ya’ya har biyu, to mai zai sa ki nemi faɗa da ita kan sha’anin kuɗi.”

A ɓangaren waɗanda ke ganin ‘yar tasa ce daidai akwai Beauty By Char, wadda ta rubuta cewa, “na fara tunanin wannan matar tasa ce matsalar, saboda na lura ba abinda take iya yi sai karvar kuɗin, kai jama’a! Mutumin nan fa bai mutu fa tukunna.”

Panache Zeal ya rubuta, ” ba don wannan yarinyar ba Jasmine, da wannan mata tasa da ta washe shi tsaf.”

Shi kuwa Nelly Vee cewa ya yi, “wannan mata da zalama take, mijinki na kwance jinya, ke kuwa tunaninki canza waya da mota ki ke yi. Tir!”

Stella Maris, matar ta Mista Ibu ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wurin mayar da martani ga ‘yar ta mijin nata, inda a nata jawabin ita ma ta tuhume ta da kutse a asusun tara kuɗaɗen na ciwon mijin nata.

“Ba ni da dama ko ikon iya yin wani abu a asusun da ake zuba tallafin a ciki wanda yake a bankin Access, inda ɗinbin mutane ke zuba tallafin su. A ƙarƙashin ƙasa Jazmine ce ke sarrafa shi, duk da haka bai ishe ta ba har sai da ta fito tana yaɗa ƙarya tare da shafa min kashin kaji, duk a ƙoƙarin ta na ganin ta ci gaba da juya asusun. Yadda ta yi shege da fice har ta samu damar juya akalan asusun kuwa labari ne na rana ta gaba,” cewar Stella.

Jaridar PUNCH a onlayin ta ruwaito cewa, ta nemi jin ta bakin Jasmine, sai dai ta tabbatar mata da cewa, ba ta da ra’ayin shiga wasan kwaikwayon kafafen sadarwa, ko da za ta yi ba yanzu ne lokacin ba, domin a yanzu hankalinta da damuwarta na kan rashin lafiyar mahaifinta. Sai dai ta nemi su gana da ɗan’uwanta, ɗan jarumin na biyu mai suna Daniel Okafor.

Daniel Okafor, ya ƙaryata zargin da matar mahaifin nasa take yi kan ‘yar’uwar tasa duk da cewa ba ciki ɗaya suka fito ba, kuma ba uba ɗaya suke tarayya ba, kuma ya tabbatar da ba wani da ke da ikon juya asusun baya ga shi.

“Sunana Daniel Okafor; kuma ni ne ɗan John Okafor na biyu. Ko kaɗan babu gaskiya a zancen da Stella Maris take yaɗawa a onlayin. Jasmine ba ta da damar juya asusun da ake tura tallafin a ciki. Ni ne mai sa hannu a asusun domin ni ne magajin mahaifinmu a hukumance a asusun,” inji shi.

Baya ga haka, Daniel ya kuma bayyana cewa, Stella Maris matar mahaifinsa ce ba ita ce ta haife shi ba, sai dai ya ƙi bayyana wani abu game da mahaifiyar tasa.”

By Editor