Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da rabon hatsi ga masu buƙata ta musamman a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya ƙaddamar da rabon buhunan hatsi mai nauyin kilogiram 100 ga masu buƙata ta musamman da matan da suka rasa mazajen su a Jihar.

Kayan abincin sun haɗa da buhunan masara ,dawa da gero buhu 30,000 kowanne.

A jawabin sa Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa wannan tallafi ba shine na farko ba, ya ce a kwanan baya gwamnati ta tallafa wa masu sana’ar koko da ƙosai da kuma tallafin kuɗi a cikin watan azumin Ramadan.

Ya ƙara da cewa gwamnatin sa ta tallafa wa mata 7,220 a faɗin jihar da shinkafa mai nauyin kilogiram 25 da naira dubu 10 kowanne su.

Gwamnan ya yaba wa Gidauniyar Dangote da ta haɗa da gwamnatin Jihar wajen tallafa wa mabuƙata da shinkafa.

Ya yi kira ga waɗanda aka basu alhakin rabon kayan abincin da su tabbatar sun yi adalci da gaskiya wajen rabon.

Haka Kuma yayi kira ga shugabannin ƙananan hukumomi,hakimai da sauran shugabannin al’umma da su sa Ido sosai tare da tabbatar da an yi gaskiya .

Waɗanda suka amfana da tallafin sun haɗa da matan da su ka rasa mazajen su,masu buƙata ta musamman,tsofaffi da masu ƙaramin ƙarfi.

By ukarofi

Leave a Reply