Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa ta cigaba da tallafa wa ƙungiyar Katsina United, tare da bunƙasa harkokin wasanni da ƙwarewar matasa a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Alhamis lokacin da ya karɓi baƙuncin shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya (NFF), Alhaji Ibrahim Musa Gusau, da sauran jami’an hukumar a fadar gwamnatin Jihar Katsina.
Gwamna Raɗɗa ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da yanayin da zai bai wa matasa damar haɓaka ƙwarewarsu a wasanni, yana mai cewa ƙwallon ƙafa na taka muhimmiyar rawa wajen haɗa kan matasa da kuma taimakawa wajen kare su daga munanan ɗabi’u.
Ya jaddada cewa tallafa wa wasanni na daga cikin hanyoyin bunƙasa matasa tare da samar musu da damammaki na amfani da ƙwarewarsu wajen gina rayuwarsu da kuma wakiltar jihar cikin nasara.
A nasa jawabin, shugaban NFF, Alhaji Ibrahim Musa Gusau, ya yaba wa Gwamna Raɗɗa bisa irin tallafin da yake bai wa ƙwallon ƙafa, musamman Katsina United da ƙwallon ƙafan matasa.
Gusau ya kuma bayyana aniyar hukumar NFF ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnatin jihar Katsina domin ci gaba da bunƙasa ƙwallon ƙafa da sauran harkokin wasanni a jihar.
