Gwamna Raɗɗa ya naɗa mataimakinsa a matsayin Amiril Hajj

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya naɗa mataimakin sa Farouk Lawal Joɓe a matsayin Amiril Hajj na tawagar maniyatan bana.

Sanarwar haka ya fito ne daga ofishin sakataren gwamnatin jihar.

Mambobin kwamitin aikin hajjin sun haɗa da kakakin majalisar dokoki RT Hon Nasiru Yahaya Daura da kwamishinan harkokin addini Ishaq Shehu Dabai.

Akwai kuma mai Shari’a Aminu Tukur ƙofar Bai da shugaban gidan rediyon Jihar Katsina Malam Lawal Attahiru Bakori.

Sauran sun haɗa da Sheikh Abu Ammar da Sheikh Nasiru Ƙofar Bari Daura da Umar Abubakar da Aliyu Hussaini

By ukarofi