Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya musanta wani zargi na musamman da wasu a jihar ke yi cewa a yanzu haka ya riga ya naɗa magajinsa a kujerar ta gwamnan jihar a zaɓukan gwamnoni da ke tafe ta shekarar 2027.
Gwamnan ya ƙaryata jita-jitar ne ta bakin mai taimaka masa a harkokin hulɗa da jama’a Kwamared Peter Ahemba a lokacin wani taron manema labarai wanda aka gudanar a cibiyar ‘yan jarida dake Lafiya babban birnin jihar ranar Laraba ta mako da ake ciki.
Gwamnan ya buƙaci al’ummar jihar bakiɗaya su yi watsi da jita-jitar wanda ya bayyana a matsayin labarin ƙanzon kurege.
Ya cigaba da bayyana cewa: “A yanzu haka kamar yadda kuka sani ina da sama da shekaru 2 a matsayin gwamnan jihar nan tamu ta Nasarawa kuma abinda ke gabanmu kawai shine cigaba da samar wa al’ummar mu ribobin dimokaraɗiyya kamar yadda muka saba.
“Saboda haka batun in zaƙulo ko naɗa magajina ba zai taɓa karkata min hankali ba a yanzu,” inji shi.
Daga nan sai gwamnan ta jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya kuma yi amfani da damar inda yayi kira ta musamman ga al’ummar jihar baki daya ciki har da ‘yan jaridan su cigaba da bai wa gwamnatin sa cikakken goyon baya don bata damar cigaba da gudanar da ayukan cigaba da take yi a yanzu a duka matakai a kuma duka fadin jihar baki daya.
A yanzu haka dai wasu a jihar ta Nasarawa dama wasu sassan ƙasar nan na cigaba da yada jita-jitar cewa duk da cewar akwai lokaci sosai kafin zaɓukan gwamnoni na shekarar 2027 mai zuwa tuni gwamnan jihar Nasarawar Injiniya Abdullahi Sule ya naɗa wanda zai gaje shi a kujerar ta sa ta gwamnan jihar a zaɓukan.
