Daga JOHN D. WADA a Lafiya
A yanzu haka hukumar fanshon Nasarawa ta kuma fara biyan ‘yan fanshon da suka yi ritaya a shekarar 2011 wato rukunin watan 1 zuwa 6 na shekarar ta 2011 kenan zunzurutun kuɗi Naira biliyan 1 wanda gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule ta sake bayarwa don biya su haƙƙinsu na gratuity da sauransu.
Babban Darakta Janar na hukumar Alhaji Suleiman Musa Nagogo ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a ofishinsa dake hukumar ranar Laraba na mako da ake ciki.
Ya ce sakin zuzuruntun kudin karo na 2 kedawuya sai hukumar batayi wata-wata ba kamar yadda ta saba ta kama aikin zakulo wadanda suka dace su amfana daga kudin na wannan karo wato ‘yan fanshon din da suka yi ritaya a shekarar 2011 rukunin watan 1 zuwa 6 a shekarar wanda gwamnatin jihar karkashin jagorancin Injiniya Abdullahi Sule ta sake bayar bayan wanda ta bayar a baya don biyan rukunin ‘yan fanshon wanda suka yi ritaya daga shekarar 1999 zuwa 2010 don rage musu kuncin rayuwa da suke fuskanta a yanzu da sauran su duk da ba gwamnatin sa ce ‘yan fanshon ke bin basussukan ba.
Darakta Janar na hukumar ‘yan fashon alhaji Suleiman Musa Nagogo ya kuma bayyana cewa tuni ma hukumar ta manna sunayen wadanda zasu amfana a karon nan a hukumar inda ta gayyace su su zo zu duba sunayen nasu sannan wadanda suka ga sunayen su din anma fara biyan su hakin su bayan tabbatar dasu inda ya kuma yi amfani da damar ya yaba wa gwamna Abdullahi Sule dangane da karamcin da gwamnatin nasa ke bai wa ‘yan fanshon rukuni-rukuni wato bayan cikakken hakin su na wata-wata da gwamnatin ke biyan su kenan inda yace tabbas hakan yana basu damar biya bukatun su dana iyalan su a yanzu.
Har ila yau Darakta Janar din Nagogo ya kuma yi amfani da damar inda ya yi kira na musamman ga waɗanda ba su samu kuɗin a wannan lokaci ko ba su yi haƙuri don ana bi rukuni-rukuni ne da zarar aka gama da na wannan karo gwamnan zai kuma cigaba har a ƙarshe kowa ya samu da yardar Allah kana ya buƙaci waɗanda suka amfana da kuɗin na bana su tabbatar sun yi amfani da kuɗin yadda ya dace don amfanar kansu da na iyalansu.
Idan ba a manta ba a farkon wannan shekarar 2024 da ake cike ma gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule ta ware irin wannan zunzuruntun kuɗi naira biliyan 1 don biya wasu rukunin ‘yan fanshon din a jihar ta Nasarawa wadanda suka yi ritaya a shekarar 1999 zuwa 2010 kamar yadda aka rubuto wasu bazassukan su da suke bi gwamnatotin tsofaffin gwamnonin jihar da suka shuɗe kafin zuwansa wato bayan biyan ‘yan fanshon kuɗaɗensu na wata-wata akai-akai kenan tun zuwansa a matsayin gwamnan jihar mai ci a yanzu.
