Kotu ta hana CBN riƙe kuɗin ƙananan hukumomin Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babbar Kotun Jihar ta hana Babban Bankin Nijeriya (CBN) da Gwmanatin Tarayya riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar 44 na wata-wata.

Kotun ta bayar da umarnin wucin gadin ne ga Gwamantin Tarayya da hukumominda ma’aikatunta, bayan ƙarar da ƙungiyar Ma’aikatan ƙananan Hukumomi ta Nijeriya (NULGE) da wasu masu kishin Jihar Kano.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Musa Muhammad, ya ba da umarnin ne ga CBN da Hukumar Rabon Kuɗaɗen Shiga na Kasa da Kuma Akanta-Janar na Tarayya kan tabawa, rikewa ko jinkirin sakin kuɗaɗen kƙananan hukumomin na jihar Kano.

Ya ba da umarnin ne kan ƙarar da masu ƙarar suka nuna damuwa cewa game da yiwuwar riƙewa ko jinkirin kuɗaɗen ƙananan hukumomin ko wani ɓangaren kuɗaɗen.

Alƙalin ya kuma umarci hukukumomin gwamantin da wakilansu da kada su kuskura su yi duk wani nau’in katsalandan kan kudaden ƙananan hukumomin.

Daga nan ya ɗage zaman zuwa ranar 21 ga watan nan na Nuwamba, 2024.

By ukarofi