Gwamna Uba ya dawo da shirin ɗaukar nauyin maniyyatan Kiristoci a Kaduna

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya dawo da shirin sauke faralin Kiristoci wanda gwamnatin jiha ke ɗaukar nauyi.

Gwamnan ya dawo da ɗaukar nauyin sauke faralin ne bayan dakatar da shirin na tsawon shekaru 11 a jihar Kaduna.

Shugabar Ma’aikata ta gwamnatin jihar Kaduna, Jimami C. Bako, ta bayyana hakan ne yayin da take jawabi a wurin taron bitar shekarar 2025 ga maniyyata Kiristoci 50 da gwamnati ta ɗauki nauyi.

Taron bitar ya nuna karon farko da jihar ta ɗauki nauyin sauke farali na Kiristoci cikin fiye da shekara 11 da dakatar da shi da gwamnatocin baya suka yi.

Shugabar ma’aikatan ta jihar Kaduna ta yaba wa Gwamna Uba Sani bisa dawo da shirin na ɗaukar nauyin sauke faralin Kiristoci.

Jimami C. Bako ta bayyana cewa gwamnatin ta amince da cewa bunƙasar ayyukan ibada da kyawawan ɗabi’u muhimman abubuwa ne da ke tafiya tare da samar da ababen more rayuwa da ci gaban tattalin arziki.

Ta ƙara da cewa, farfaɗo da shirin sauke faralin ya nuna irin salon shugabanci ne da ke ɗaukar addini a matsayin ginshiƙin zaman lafiya da haɗin kan al’umma.

Kwamishinan yaɗa labarai, Ahmed Maiyaki, ya bayyana cewa wannan matakin ya yi daidai da ƙudurin gwamnatin na samar da adalci, daidaito, da kuma tafiya tare da kowa da kowa ba tare da la’akari da addini ba.

Kwamishinan ya buƙaci maniyyatan da su yi amfani da wannan dama su yi addu’ar neman zaman lafiya, haɗin kai, da ɗorewar arziki a jiha da ma kasa baki ɗaya.

Ga waɗanda suka amfana, dawo da shirin sauke faralin ya zama alama ta sabon fata, ƙarfafa amincewa ga gwamnatin jiha, da kuma ƙarfafa zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-daban a Kaduna.

A watan Nuwamba na shekarar 2014, maniyyatan Kiristoci 567 daga Kaduna ne aka kwashe daga filin jirgin saman jihar zuwa ƙasar Isra’ila.

Yayin da ya ke jawabi a filin jirgin saman lokacin da suke tashi, Ramalan Yero, wanda shi ne gwamnan jihar a lokacin, ya buƙaci maniyyatan da su kasance jakadu nagari na Nijeriya yayin da suke a Isra’ila.

By ukarofi