Tinubu ya sa hannu kan umarnin tura kuɗin ɗanyen mai Asusun Tarayya kai tsaye

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan wani muhimmin umarni na zartarwa da zai tabbatar da cewa dukkan kuɗaɗen shiga daga ɓangaren mai da iskar gas ana tura su kai tsaye zuwa Asusun Tarayya, wato Federation Account.

Mai ba Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar 18 ga Fabrairu, 2026.

Ya ce, an ɗauki matakin ne domin karewa da kuma ƙara haɓaka kuɗaɗen shiga daga mai da gas, rage almubazzaranci, kawar da tsarin da ke maimaita juna a fannin tattalin arziki, tare da mayar da albarkatun ƙasa zuwa amfanin al’ummar Nijeriya.

Onanuga ya bayyana cewa Shugaban ƙasa ya sanya hannu kan umarnin ne bisa ikon da Sashe na 5 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya ba shi. 

Haka kuma, umarnin ya dogara da Sashe na 44(3) na Kundin Tsarin Mulkin, wanda ya tanadi cewa mallaka da iko da dukkan ma’adanai, man fetur da iskar gas a Nijeriya na hannun Gwamnatin Tarayya ne.

Ya ƙara da cewa, wannan mataki na da nufin dawo da haƙƙoƙin rabon kuɗaɗen shiga na gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi, waɗanda aka ce Dokar Masana’antar Mai (PIA) ta shekarar 2021 ta rage musu.

ɗaya daga cikin muhimman sauye-sauyen da umarnin ya ƙunsa shi ne soke tsarin cire kashi 30 na ribar haɗin gwiwa (Profit Sharing) da ake warewa don asusun binciken sabbin wuraren mai (Frontier Eɗploration Fund). A ƙarƙashin sabon tsarin, kamfanin NNPC ba zai sake tara ko sarrafa wannan kashi 30 ba, kuma ba zai ƙara karɓar kuɗin gudanarwa kan ribar mai da gas ba.

Dukkan kuɗaɗen Royalty Oil, Taɗ Oil, Profit Oil, Profit Gas da sauran kuɗaɗen da suka wajaba daga kwangilolin haɗin gwiwa za su riƙa shiga kai tsaye zuwa Asusun Tarayya daga ranar 13 ga Fabrairu, 2026.

Haka zalika, Shugaban ƙasa ya dakatar da biyan kuɗin tara da ake karɓa kan ƙona gas (Gas Flare Penalty). Daga yanzu, duk waɗannan kuɗaɗe za su riƙa shiga kai tsaye zuwa Asusun Tarayya, tare da tabbatar da cewa duk wani kashe kuɗi daga asusun zai bi dokokin sayen kayayyaki na gwamnati.

Shugaba Tinubu ya kuma bayyana aniyar sake duba Dokar Masana’antar Mai (PIA) tare da tuntuɓar masu ruwa da tsaki domin gyara kura-kuran tsarin kuɗi da tsarin gudanarwa da aka gano.

Haka kuma, an amince da kafa kwamitin aiwatarwa wanda zai haɗa da Ministan Kuɗi, Ministan Shari’a, Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare, ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, Shugaban Hukumar Haraji ta ƙasa, da sauran manyan jami’ai domin tabbatar da aiwatar da umarnin yadda ya kamata.

Sanarwar ta jaddada cewa wannan gyara na da matuƙar muhimmanci ga kasafin kuɗin ƙasa, ɗorewar biyan basussuka, daidaiton tattalin arziki da kuma walwalar ‘yan Nijeriya. Gwamnati ta ce manufar ita ce ƙara gaskiya, rage giɓin kuɗaɗen shiga, da tabbatar da cewa ana amfani da albarkatun ƙasa domin ci gaban ƙasa baki ɗaya.

By ukarofi