Gwamna Yusuf zai samar da wuta mai amfani da hasken rana a makarantu 200 na Kano 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da wani babban shiri na haskaka makarantu 200 na gwamnati da wuta mai amfani hasken rana tare da samar da kwamfutoci 250 ga kowacce makaranta a ƙarƙashin shirin AGILE da Bankin Duniya ke tallafawa.

Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati wajen gyara bangaren ilimi da rage gibin fasaha a fadin jihar.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne a lokacin bikin ƙaddamar da rabon kayan koyarwa ga makarantun firamare da na sakandare da aka gudanar a Kano.

A cewar gwamnan, samar da wutar lantarki ta hasken rana zai ba makarantu damar samun wuta mai ɗorewa, wanda zai taimaka wajen inganta yanayin koyarwa ta zamani.

Kwamfutocin da za a raba ana sa ran za su ƙara damar amfani da fasaha da kuma inganta ingancin ilimi ga dubban ɗalibai.

“Manufarmu ita ce mu kawar da giɓin fasaha domin tabbatar da cewa ɗalibanmu ba a bar su a baya ba a wannan zamani na ci gaban kimiyya da fasaha,” inji Gwamna Yusuf.

By ukarofi