Gwamnan Akwa Ibom ya bayyana ɗiyar shi a matsayin wadda za ta maye gurbin ofishin matar gwamna

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya nada ɗiyar sa, Helen Eno-Obareki, a matsayin wadda za ta riƙe ofishin matar gwamna na riƙo, bayan rasuwar matarsa ​​Fasto Patience Eno.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a yayin ziyarar ta’aziyya da uwargidan shugaban Nijeriya, Sanata Oluremi Tinubu da wasu jiga-jigan ƙasar suka kai a Uyo.

A cewar gwamnan, ɗiyar sa za ta ɗauki nauyin aikin ofishin matar gwamna, tare da tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan da marigayiyar matarsa ​​ta ƙaddamar, musamman na Golden Initiative For All.

Don in kula da Ofishin matar gwamna kuma in ci gaba da aikin matata da ta rasu, ina ba wa ’yarmu, Helen, don ta ci gaba da hidima a ofishin. Za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da mataimakin gwamna da kwamishiniyar harkokin mata da walwalar jama’a,” inji gwamnan.

Ya bayyana ƙwarin gwiwarsa kan yadda ‘yarsa za ta iya kiyaye ɗabi’u da hangen nesa na mahaifiyarta marigayiya, yana mai tabbatar da ƙudurin sa na ci gaba da gudanar da ayyukan da aka fara a ofishin matar gwamnan.

Ya nanata cewa rashin matarsa ​​marigayiya ba zai iya maye gurbin ta ba, kuma ya mayar da hankali wajen ganin ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na ofishin matar gwamnan.

By ukarofi