Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina malam Dikko Raɗɗa ya yi ta’aziya ga iyalan jami’an tsaron da ‘yan bindiga su ka kashe a ƙaramar hukumar Faskari.
Jami’an tsaro guda shida suka rasa rayukansu a yayin da suke fafatawa da ‘yan bindiga a kan hanyar Yankara zuwa Faskari.
Sun kuwa haɗa da jami’an tsaro na al’umma (community watch corps) su huɗu da ‘yan banga biyu.
Ya bayyana su a matsayin jarumai da suka sadaukar da rayukan su wajen kare rayukan al’umma.
A wata takardar sanarwar ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labarai na gwamnan kaula Muhammad, Mallam Dikko Raɗɗa ya bayyana jami’an tsaron da suka mutu a matsayin waɗanda suka yi shahada.
Gwamnan ya kuma yabawa sauran jami’an tsaro na ‘yan sanda da sojoji bisa ƙara ƙaimi da suke nunawa wajan kakkaɓe ‘yan bindiga a yankin.
Malam Dikko Raɗɗa ya kuma sha alwashin kamo waɗanda suka aikata wannan ta’addan ci domin a hukunta su
