An shiga halin ɗar-ɗar kan rashin tabbas ga makomar ministocin Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Alamu masu ƙarfi sun nuna cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kammala jaddawalin sunayen ministocin da za su cigaba da aiki da shi bayan garambawul ga tawagar ma’aikatansa.

Bayanai da dama a Fadar shugaban ƙasa sun ce, Tinubu ya kammala aikin jaddawalin inda aka cire wasu da kuma barin waɗanda za a cigaba da tafiya da su, wanda an yi tsammanin ya fitar a ranar Alhamis, kwana ɗaya kafin ya tafi hutu Birtaniya, kamar wani da ya nemi a sakaye sunansa ya bayyana.

Sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a watan Agusta ne, Tinubu ya fara fuskantar matsi daga ciki da wajen jam’iyyarsa ta APC kan cewa ya tsige ministocin da basa aiki yadda ya kamata a gwamnatinsa.

Duk da cewa shugaban ƙasar ya sha gargaɗin ministocin kan rashin tsare ayyukansu, hakan bai sa ya sallami koɗaya daga cikin su ba in ban da dakatar da Ministar Ma’aikatar Jin-ƙai, Dakta Betta Edu da ya yi a watan Janairun 2024.

A Nuwamban 2023 ne Tinubu ya naɗa tawagar sanya ido kan ayyukan ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati wanda mai ba shi shawara kan Tsare-Tsare, Hadiza Bala Usman ke jagoranta yayin da rahotonsu shi zai nuna wanda ya kamata a tafi da shi da kuma waɗanda ya kamata a tsige.

An ruwaito cewa, wasu daga cikin ministocin za a yi musu sauyin wuraren aiki yayin da za a haɗe wasu ma’aikatun da kuma rushe wasu.

A ranar 25 ga watan Satumba ne aka tabbatar da cewa Shugaba Tinubu zai yi wa ministocinsa garambawul.

By Babaji