Daga USMAN KAROFI
Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya biya bashin Naira biliyan 9,357,743,281.35 ga ma’aikatan jihar da su kayi ritaya daga shekarar 2011.
Gwamnan ya amince da fara biyan giratutin tun watan Fabrairun wannan shekara.
Hakan ya fita ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris ya fitar, in da ya tabbatar da biyan wannan kuɗaɗe a cikin rukuni tara.
Ya cigaba da cewa wannan kaɗan ne daga cikin irin sauye-sauye da gwamnan ke ƙokarin kawo wa ma’aikatan gwamnatin jihar inda ya umarci sake tantance wanda su kayi ritaya tun daga shekarar 2011.
A yanzu haka aƙalla ‘yan fansho 2,666 daga cikin 3,880 da aka tantance an biya su haƙƙoƙinsu.
Haka zalika, ‘yan fansho 3,840 daga cikin 4804 da aka tantance waɗanda sun kasance ma’aikatan ƙananan hukumomi da malaman firamare su ma an biya su haƙƙoƙinsu.
Wannan ya nuna irin jajircewa da kuma dagewa da gwamnan ya ke yi domin ganin an samu canji a kan yadda lamura ke faruwa musamman abinda ya shafi giratutin ma’aikatan da su kayi ritaya.
