Gwamnan Kano ya dakatar da mashawarcinsa bisa sukar Kwankwaso

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin gaggawa na a dakatar da babban maruwaici na musamman (SSR) a Ma’aikatar Sufuri, Ibrahim Rabi’u kan kalamansa masu fusatarwa.

Haka kuma Gwamnan ya umarci a ba shi takardar amsar laifi a sakamakon yin kalamai masu fusatarwa akan yiwuwar ficewar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso daga Jam’iyyar NNPP.

Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim ya fitar da takardar dakatarwar a ranar Lahadi.

Kakakin Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa a wata takarda, ya ce gwamnatin ta gargaďi dukkan masu mukaman siyasa akan yaɗa kalaman da ba a amince da su ba, inda sai an tabbatar tare da amincewa da kowane batu kafin yaɗa shi acikin al’umma.

Ya bayyana cewa, gwamnatin ta nesanta kanta daga kalaman dakataccen jami’in, yana mai cewa suna wakiltar sa ne bisa wasu dalilai da shi ya san su.

Gwmanatin jihar ta kuma tunatar da al’umma cewa Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin gida, Kwamared Ibrahim Wayya shi ne wanda aka amince ya yi magana kai-tsaye a madadinta, sa kuma Daraktan labarai da Hulda da Jama’a, Sanusi Bature a madadin Gwamnan.

By Babaji