Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya halarci ɗaurin auren ɗan Kwamishinan Ilimi na jihar, Gwani Ali Haruna Makoɗa, da aka gudanar a Masallacin Sheikh Isyaka Rabiu da ke Gauron Dutse, a makon da ya gabata.
Gwamna Yusuf, wanda ya tsaya a matsayin waliyyin ango, Abdufattah Gwani Ali Makoɗa, tare da amaryarsa Maryam Sa’id Muhammad, ya jaddada muhimmancin aure a matsayin ginshiƙin samun zuriyar albarka. Ya taya ma’auratan murna tare da yi musu addu’ar zaman lafiya, albarka, da yalwar arziki mai dorewa, inda ya kuma shawarce su da haƙuri da juna da girmama junansu a wannan sabon matakin rayuwa.
A nasa jawabin, uban ango, wanda kuma shi ne Kwamishinan Ilimi, Gwani Ali Haruna Makoda, ya bayyana farin cikinsa da godiya ga Allah da ya nuna musu wannan rana. Ya yi kira ga ma’auratan da su kasance masu nuna soyayya da kauna a tsakaninsu, tare da haƙuri da juna domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.
Haka zalika, mai ba wa Gwamnan shawara kan harkokin tsare-tsaren siyasa kuma tsohon shugaban ƙaramar hukumar Doguwa, Hon. Ali Audu Doguwa, ya taya ma’auratan murna tare da yi musu addu’ar samun zuriyar albarka. Ya ƙara da jan hankalin su da su kasance masu nuna haƙuri da girmama junansu domin ɗorewar zaman lafiya a aurensu.
Shi kuwa angon, Abdufattah Gwani Ali Haruna Makoɗa, ya bayyana farin cikinsa ga Allah da ya basu damar shiga wannan sabon mataki bayan dogon jira. Ya gode wa mahalarta daurin aure, tare da yi musu fatan alkhairi da addu’ar Allah ya maida kowa gida lafiya.
ɗaurin auren ya samu halartar manyan mutane ciki har da Gwamnan Jihar Kano, kwamishinoni, masu ba wa gwamnati shawara, ‘yan siyasa, da sauran jami’an gwamnati daga matakin jiha da kuma ƙaramar Hukumar Makoɗa.
