Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da shirin koyar da sana’o’in dogaro da kai ga matasa a garin Getso da ke ƙaramar Hukumar Gwarzo.
Da yake jawabi yayin bikin buɗe cibiyar, babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Kano, Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa, wanda ya jagoranci wakilan cibiyar jami’an yaɗa labarai da hulɗa da jama’a (NIPR) domin sheda ƙaddamar da bayar da horon da kuma ganewa idanun su wasu ayyuka da gwamnatin jihar Kano take aiwatarwa, ya bukaci wadanda zasu amfana da shirin su mayar da hankali kan sana’o’in da za a koya musu.
Ya ce gwamnatin Kano ƙarƙashin Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta himmatu wajen hidimtawa al’umma da bunƙasa cigaban matasa da ba su jari.
A nasa angaren, shugaban Jam’iyar NNPP na karamar hukumar Gwarzo, Alhaji Abdulkadir Ahmad Getso, ya ce an debi kashin farko na matasa fiye da 200 da suka haɗa da maza da mata ‘yan asalin ƙaramar hukumar.
Hon Getso ya ce za a fara koyar da matasan ɗinkuna na zamani daga bisani kuma a tallafa musu da jari domin su dogara da kawunansu.
Abdulkadir Getso, ya ƙara da cewa, matasan zasu kwashe makonni takwas suna ɗaukar hoto, da zarar sun kammala kuma za a sake ɗaukar wasu sabbin ɗaliban da za su amfana.
