Gwamnan Kano ya kori Sagagi, Bichi da Ɗantiye daga gwamnatinsa

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi garambawul a Majalisar Zartarwarsa. Mai magana da yawun gwamnan na Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai jiya Alhamis.

Sanarwar ta ce, gwamanan cire Shugaban Ma’aikata na Fadar Gwamnatin Jihar Kano, Shehu Sagagi, da Kwamishinan Yaɗa Labarai, Halilu Dantiye, da kuma Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Baffa Bichi, wanda shi saboda rashin lafiya ne aka sauke shi, sannan kuma ya rushe Ofishin Shugaban Ma’aikatansa, Shehu Wada Sagagi.

Sauran kwamishinonin da aka sauke sun haɗa da Kwamishinan Kuɗi Ibrahim Jibril Fagge da Shehu Aliyu Yammedi Kwamishinan Ayyuka na Musamman, sai kuma Abbas Sani Abbas na Ma’aikatar Raya Karkara da Ladidi Ibrahim Garko Kwamishiniyar Al’adu da Yawon Buɗe Ido.

Haka zalika Gwamna Abba ya kuma sauya wa wasu daga cikin kwamishinonin ma’aikatu. Waɗanda canjin ya shafa sun haɗa da Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da yake riƙe da Ma’aikatar ƙananan Hukumomi yanzu ya koma Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, sai Hajiya Amina Abdullahi HOD daga Ma’aikatar Jinƙai zuwa Ma’aikatar Mata, Masu Buƙata ta Musamman da Yara.

Sauran sun haɗa da Hon. Muhammad Tajo daga Ma’aikatar Fasaha da ƙirƙira zuwa Ma’aikatar ƙananan Hukumomi, haka kuma Hon. Aisha Lawan Saji daga Ma’aikatar Mata da Masu Buƙata ta Musamman zuwa Ma’aikatar Al’adu da Yawon Buɗe Ido, sai Hon. Ali Haruna Makoda daga Ma’aikatar Samar da Ruwa zuwa Ma’akatar Ilimi.

Sauran sun haɗa da Muhammad Tajo daga Ma’aikatar Fasaha da ƙirƙira zuwa Ma’aikatar ƙananan Hukumomi, Sai Hon Namadi Dala daga Ma’aikatar Bibiyar ayyuka zuwa Ma’aikatar Sufuri, sai Hon. Muhammad Diggol Daga Sufuri zuwa Ma’aikatar Bibiyar Ayyuka, Nasiru Sule Garo daga Ma’aikatar Kula da Muhalli da Yanayi zuwa Ayyuka na Musamman.

Haka zalika gwamnan ya kuma mayar da Yusuf Ibrahim Mata da ke matsayin Kwamishina na Ilimi mai Zurfi zuwa Ma’aikata Fasaha da ƙirƙira.

Wasu daga cikin waɗanda suka samu damar cigaba da zama ma’aikatun su, sun haɗa da Hamza Safiyanu Kachako na Ma’aikatar Kula da Ma’adanai, sai Mustapha Rabiu Kwankwaso Ma’aikatar Wasanni da Matasa, sai Hon Adamu Aliyu Kibiya na Ma’aikatar Kasuwanci da Zuba Jari tare da Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro ta Cikin Gida Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris mai ritaya.

Sauran waɗanda abin bai shafa ba su ne Kwamishina Ma’aikatar Addinai da Kwamishinan Shari’a Barista Haruna Isa Dederi sai kuma Kwamishinan Ma’aikatar Tsimi da Tanadi Hon. Musa Suleiman Shanono tare da Kwamishinan Ma’aikata Gona Dr. ɗanjuma Mahmood, sannan shi ma Hon Abubukar Labaran na Ma’aikatar Lafiya da Hon Abduljabbar Umar Garko na ƙasa da Safiyo sun tsira da kujerunsu.

Wakilin Blueprint Manhaja ya ruwaito mana cewa, gwamnan ya umarci kwamishinonin guda biyar da ya sauke su garzaya ofishinsa, domin duba yiwuwar ba su wasu ayyukan.

By ukarofi