Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
‘Yan kasuwa a Kano sun koka da cewa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya yi watsi da su tun bayan da ya lashe zaɓen 2023.
‘Yan kasuwar, ta bakin Munzali Abubakar Dambazau, wanda shi ne jagoran ƙungiyar Abba na Kowa a Kano, ya ce tuni ‘yan kasuwa, musamman na kasuwar Kantin Kwari su ka fara gunaguni kan cewa gwamnan ya yi watsi da su.
Da ya ke magana a shirin Kowanne Gauta na Freedom Radio, Dambazau ya ce, a lokacin zaɓen gwamna sanya gabata, ‘yan kasuwar Kwari sun bada gudunmawar atamfuna da shaddoji da kudade don ganin Abba ya samu nasara, inda ya ƙara da cewa “lamarin na neman zama cewa mun tura mota amma ta buɗe mu da hayaƙi.”
“Yan kasuwa da dama su na ƙorafi. Mu ne mu ke tare da su kuma mu ne wakilan gwamna a kasuwanni, dole ne idan muka ji ko mu ka ga wani abu na ba dai-dai ba dole mu jawo hankalin mai girma Gwamna.
“Mu na kira ga gwamna da Jagora, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, da su dubi yan jam’iyya, musamman ‘yan kasuwa da ya cika alkawaran da ya ɗaukar wa ‘yan kasuwa, musamman ma kasuwar Kwari.
“Shi ya sa mu ke kira ga gwamnan Abba mai adalci da ya saurari koken nan na dubban ‘yan kasuwa a jihar Kano,” inji Dambazau.
