Gwamnan Kwara ya kaɗa ƙuri’a, ya nuna damuwa kan na’urar BVAS

Daga WAKILINMU

Bayan jinkirin da aka samu na zuwan kayan aikin zaɓe a mazaɓarsa, a ƙarshe Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara ya samu kaɗa ƙuri’arsa.

Gwamnan ya jefa ƙuri’ar tasa ce a mazaɓarsa mai lamba 004 da ke gundumar Adewole a Ilorin ta yamma.

Ya nuna damuwarsa kan ƙalubalen da aka fuskanta na rashin aikin na’urar BVAS a wasu sassan jihar.

Kana ya yaba wa ƙoƙarin jami’an tsaro da kuma yadda jama’a suka fito a jihar don jefa ƙuri’arsu.

A ƙarshe, Gwamnan ya bayyana yaƙininsa na cewa ko shakka babu APC za ta yi nasara.