Ƙalubalen da ke gaban shugaban Nijeriya da za a zaɓa

Kasancewarta mafi girman tattalin arziki kuma mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka, mai sama da mutum miliyan 214, hakan ya sa duk wani abu da ya faru a Nijeriya yake yin tasiri a faɗin nahiyar.

Masu kaɗa ƙuri’a za su zaɓi sabon shugaban ƙasa bayan kwashe shekara takwas ƙarƙashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, sai dai duk wanda ya yi nasara akwai wasu manyan ƙalubale da zai yi fama da su.

A wannan ra’ayin, jaridar Blueprint Manhaja za ta kawo maku wasu muhimman abubuwan da suka fi damun masu kaɗa ƙuri’a.

A shekarar da ta gabata, kamar sauran al’ummar duniya, ’yan Nijeriya sun fuskanci matsalar hauhuwar farashin kayan abinci saboda rikicin Ukiren. To amma farashin ya fara tashi ne tun kafin yaƙin Ukiren, bayan da gwamnati ta rufe iyakokin qasar domin hana shigar da wasu kayayyaki. Sai kuma matsalar ƙarancin dala.

An kiyasta cewa an samu tashin farashi a shekara ta 2022 da kimanin kashi 19 cikin ɗari mafi muni ke nan da aka samu cikin shekara 20. Garin rogo na ɗaya daga cikin abubuwan da tashin farashin bai shafa ba sosai, to har yanzu iyalai na jin raɗaɗin tashin farashin abubuwa kamar tumatir da man girki.

Idan sabon shugaban ƙasar na son ya taimaka wa mutane kan rage raɗaɗin farashin abubuwan da suke buƙatu na yau da kullum, to zai fuskanci ƙalubalen cewa yanzu haka gwamnati na kashe fiye da abin da ta ke samu.

Ana kashe maƙudan kuɗaɗe kan tallafin man fetur, kuma ƙasar mai arzikin man fetur ta gaza cin gajiyar tashin farashin fetur a duniya kasancewar ba ta iya tace fetur na a-zo-a gani a cikin gida ba, wanda dole sai ta sayo tataccen man fetur daga waje.

Masu sharhi na damuwa kan ko ƙasar za ta iya ci gaba da biyan bashin da ake binta, ganin cewa a wasu lokutan cikin shekarar 2022 kuɗin ruwa kawai na bashin da ake binta ya fi ƙarfin abin da take samu.

A matsayinta ta ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi fitar da ɗanyen mai a nahiyar Afirka, Nijeriya na dogaro da ɗanyen man ne wajen samun kuɗaɗen shiga da kuma kuɗin ƙasashen ƙetare. Sai dai ƙasar ta kasa cin gajiyar kuɗaɗen da take samu daga ɗanyen man, an sace yawancin kuɗin, wasu kuma an yi wadaƙa da su.

Haka nan kuma yawan man da ƙasar ke haƙowa na raguwa a cikin shekara 10 da ta wuce. A 2022 yawan man da ake fitarwa ya yi ƙasa fiye da kowa ne lokaci a cikin shekara 30.

An ɗaro mafi yawan laifin a kan satar ɗanyen mai da masu farfasa butun mai. Hakan ɗori ne a kan shekarun da aka kwashe ba tare da zuba isasshen jari a ɓangaren ba, wanda hakan ya sa ƙasar ke komawa baya cikin jerin ƙasashen Afirka da ke fitar da man fetur a nahiyar Afirka.

Kasancewar rabin yawan al’ummar Nijeriya matasa ne ’yan ƙasa da shekara 18, sabon shugaban Nijeriya zai fuskanci ƙalubalen yadda zai ci gajiyarsu a mulkinsa.

Suna buƙatar bayar da gudunmawa wajen taimaka wa bunƙasar tattalin arziki da kuma burin al’ummar mai tasowa.

Duk da cewa akwai mutane da dama waɗanda shekarunsu ba su kai na zaɓe ba, kashi 40 na masu kaɗa ƙuri’ar suna da shekaru ƙasa da 35 ne. Samun goyon bayansu zai iya yin tasiri a sakamakon zaɓen.

Abu na farko da matasan Nijeriya suke so shi ne aikin yi.

Yanzu haka kashi uku cikin huɗu na al’ummar Nijeriya ba su da aiki. A ɓangaren matasa, sama da rabi na ’yan shekara 15 zuwa 24 suna neman aikin yi.

Tabbas matakan yaƙi da cutar Korona sun taka rawa, to amma yawan marassa aikin yi a ƙasar na ƙaruwa tun kafin vullar cutar Korona.

Tattalin arzikin ƙasar na samun cigaba tun 2015, sai dai ba ya bunqasa da sauri ta yadda zai samar da aiki ga duk masu neman aikin.

Ana ɗora wani ɓangare na laifin rashin bunƙasar tattalin arzikin a kan rashin tsaro, amma masana tattalin arziki na ganin cewar ƙarancin kuɗaɗen ƙetare da rufe iyakokin ƙasar sun sanyaya wa masu zuba jari gwiwa.

Akwai ƙarancin wadatuwar abubuwan buƙatu na yau da kullum waɗanda za su iya bunƙasa rayuwa da harkar kasuwanci.

An daɗe ana suka kan ƙarancin lantarki na ƙasar, alƙaluman Bankin Duniya sun nuna cewa ƙasa da kashi 55 na al’ummar ƙasar ne ke samun wutar lantarki.

Idan aka koma ɓangaren masu amfani da intanet kuwa, kashi 36 ne kacal na al’ummar Nijeriya suke iya shiga intanet, wanda hakan ya sa ta zamo daidai da sauran ƙasashen Yammacin Afirka.

Magance ƙaruwar matsalar tsaro a Nijeriya shi ma babban ƙalubale ne ga sabon shugaban ƙasar.

Lokacin da aka zaɓi Shugaba Buhari karon farko a 2015, babbar matsalar tsaron da ake fuskanta ita ce ta Boko Haram wadda ke addabar Arewa maso Gabas. Duk da cewa yanzu Boko Haram ba ta riƙe da wani yanki na ƙasar, ƙaruwar garkuwa da mutane, da hare-hare masu alaƙa da siyasa, da rikicin manoma da makiyaya, da na ’yan bindiga, da kuma amfani da ƙarfi fiye da kima daga jami’an tsaro na sanyaya gwiwar al’umma game da ikon gwamnati na tsaron lafiyarsu.

A yanzu matsalar ta yaɗu zuwa faɗin ƙasar, ba Arewa maso Gabas kawai ba.

Ɗaya daga cikin yara biyar waɗanda ba sa zuwa makaranta a faɗin duniya daga Nijeriya suke, kamar yadda Asusun Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF ya bayyana.

Kasancewar kusan kashi 40 na yara ’yan shekara 5 zuwa 11 ba sa zuwa makaranta, lamari ne mai tayar da hankali.

Wannan matsala ce da ta shafi kowane ɓangare na ƙasar, to amma ta fi ƙamari ne a arewacin ƙasar. Matsalar tsaro na daga cikin abubuwan da suka ta’azzara lamarin, sai dai talauci da kuma bambancin jinsi na taka muhimmiyar rawa.