Gobara ta tashi a kasuwar Monday Market a Maiduguri

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Maiduguri

Babbar kasuwar Maiduguri wadda aka fi sani da Monday Market tana ci da wuta, sakamakon tashin gobara da safiyar Lahadi.

Ya zuwa haɗa wannan rahoto an ga ma’aikatan kashe gobara na ƙoƙarin daƙile yaɗuwar wuta zuwa sassan kasuwar.

Daraktan Hukumar Kwana-kwanan a jihar, Umaru Kirawa, ya tabbatar da aukuwar gobarar sa’ilin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN).

Ya ce ma’aikatan kashe gobara na jihar tare da haɗin gwiwar takwarorinsu suna aiki tukuru wajen shawo kan gobarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *