Daga SANI AHMAD GIWA abuja
Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya sha kaye a rumfarsa ta gundumar Angwan Rimi, GRA A1, da ke ofishin LERCEST da ke garin Keffi a Jihar Nasarawa, a zaɓen Shugaban Ƙasa da aka gudanar ranar Asabar, inda Jam’iyyar Labour ta yi nasara.
Peter Obi na Jam’iyyar Labour ne ya yi nasara a akwatin da ƙuri’u 132 yayin da APC ta zo ta biyu da ƙuri’u 85.
Wannan lamari dai na zuwa ne jim kaɗan bayan da Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya sha kaye a hannun Jam’iyyar Labour shi ma.
A rumfar zaɓen da ke makarantar firamare ta Elizabeth Fowler, Unit 14, gundumar G2, Masha Surulere, Obi ya samu ƙuri’u 89 inda ya doke Tinubu wanda ya samu ƙuri’u 59, yayin da Atiku ya samu ƙuri’u 5.
A wata sabuwa kuma, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour Party (LP), Datti Baba-Ahmed, ya sha kaye a hannun Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP.
