Gwamnan Wasit ya sauka daga mulki bayan gobarar kasuwa ta hallaka mutane 60 a Iraƙi

Spread the love

Gwamnan lardin Wasit da ke ƙasar Iraƙi, Mohammed al-Miyahi, ya ajiye muƙaminsa a ranar Laraba, mako guda bayan wata gobara mai muni ta tashi a cikin wata sabuwar kasuwa a garin Kut, inda ta hallaka mutane fiye da 60, tare da jikkata wasu da dama.

Gobarar ta faru ne a ranar Laraba da ta gabata a cikin wani sabon katafaren cibiyar kasuwanci (shopping mall), wacce ba ta da isassun matakan tsaro, kamar yadda mazauna yankin da jami’ai suka bayyana. Bincike na ci gaba da gudana, sai dai al’ummar yankin da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu sun nuna cewa rashin tsari da cin hanci sun daɗe suna hana ɗaukar matakan da suka dace.

A cikin sanarwarsa ta murabus, Gwamna Mohammed al-Miyahi ya ce: “Na yanke shawarar ajiye wannan muƙami ne a matsayin girmamawa ga jinin shahidai. Domin lallai suna buƙatar wani abu da zai sauƙaƙa musu raɗaɗin da suke ciki. Wannan kuma alamar biyayya ce ga su da kuma al’ummar wannan lardi.”

Bayan murabus ɗinsa, Majalisar Lardin Wasit ta zaɓi Hadi Majid Kazzar a matsayin sabon gwamna na lardin.

Gobarar ta haifar da zanga-zanga mai zafi a faɗin yankin, inda ‘yan uwa da dangin waɗanda suka mutu suka buƙaci a sauke gwamnan, tare da gurfanar da duk waɗanda ke da hannu a sakacin da ya haifar da gobarar. Mafi yawan jama’a sun danganta haɗarin da ya faru da daɗaɗɗiyar matsalar cin hanci da rashin nagartaccen duba da aka daɗe ana yi wa ɓangaren gine-gine a ƙasar.

Wannan lamari na daga cikin jerin manyan gobara da suka ta’azzara a Iraƙ cikin shekarun baya-bayan nan, wanda ke ƙara jefa tambaya kan yadda tsaron rayuka da dukiyoyi ke taɓarɓarewa sakamakon cin hanci, sakaci, da lalacewar tsarin mulki.

“Za mu ci gaba da bin lamarin har sai an hukunta duk wanda aka samu da laifi,” inji wani daga cikin masu zanga-zanga a wajen ginin da gobarar ta faru.

Gwamnatin tarayya ta Iraƙi har yanzu ba ta fitar da cikakken rahoton bincike ba, sai dai an yi alƙawarin za a gudanar da bincike mai zurfi, kuma za a ɗauki matakan hukunta waɗanda suka yi sakaci.

Wannan murabus na Gwamna al-Miyahi ya zo ne a daidai lokacin da ake ta samun ƙaruwar matsin lamba daga jama’a kan yadda ake tafiyar da lamuran tsaro da gine-gine a ƙasar.

A baya-bayan nan ma, an samu irin wannan matsala a wasu birane da dama na Iraƙ, inda gobara ke laƙume gine-gine saboda rashin matakan kare gobara da rashin bin ka’idojin tsaro.

By ukarofi