Harin Isra’ila ya hallaka dangi guda suna cikin barci a Gaza

Spread the love

Harin sama da Isra’ila ta kai da sassafe ya halaka wani iyali gabaɗaya a birnin Gaza, yayin da suke cikin barci kuma ba su ci komai ba. Dangin da aka kashe sun haɗa da Wala al-Jaabari, wata ‘yar jarida mai zaman kanta, mijinta da yara guda biyar.

Lamarin ya faru a unguwar Tel al-Hawa da ke Gaza City, inda gawarwakin iyalin aka ciro su daga baraguzan gida, aka shimfiɗa su a waje cikin farin zanen gawa da rubuce-rubuce da sunayensu. “Wannan ɗan uwana ne, yana da shekara 10. Mun ciro su da hannunmu daga ƙasa,” inji Amr al-Shaer, ɗaya daga cikin ‘yan uwansu.

A cewar Iman al-Shaer, wani ɗan uwa da ke zaune a makwabtaka da su, yaran sun kwanta barci ba tare da sun ci abinci ba. “Yaran sun kwanta da yunwa, sannan rokokin suka faɗo,” inji shi.

Isra’ila ba ta ce komai kan harin gidan ba, amma ta bayyana cewa ta kai farmaki kan “cibiyoyin ‘yan ta’adda” guda 120 a Gaza cikin sa’o’i 24 da suka wuce. Harin ya ƙara yawan mace-macen fararen hula, inda rahotanni daga asibitoci suka nuna an kashe fiye da mutane 100 a cikin awa guda 24.

A daidai lokacin da ake fama da hare-hare, rahotannin sun nuna cewa, mutane 10 sun mutu daga yunwa cikin dare, lamarin da ya kai yawan mace-mace daga yunwa zuwa 111, mafi yawan su yara.

ƙungiyar WHO ta bayyana cewa, yara 21 da ƙasa da shekaru 5 ne suka mutu daga rashin abinci a bana, tare da yin kira ga Isra’ila da ta sassauta hanyoyin shigar kayan agaji. ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa da dama sun nuna damuwa da yadda ake hana su shiga domin kai abinci da magunguna.

Wasu maƙwabta na dangin da aka kashe sun tsira ne kawai domin sun fita neman abinci da dare kafin rokokin su faɗo.

Duk da irin waɗannan hare-hare, ana ci gaba da ƙoƙarin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas. Hamas ta miƙa amsarta ga masu shiga tsakanin ƙatar da Masar dangane da wani sabon tayin tsagaita wuta na kwanaki 60 da zai haɗa da sakin fursunoni.

Sai dai har yanzu akwai saɓani a kan batutuwan da suka haɗa da: yadda za a fitar da dakarun Isra’ila daga Gaza da kuma yadda za a raba kayan agaji yadda ya dace.

Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya ziyarci Gaza inda ya ce: “Ana ci gaba da tattaunawa sosai don dawo da fursunonin da ke hannun Hamas. Muna fatan jin labari mai daɗi nan ba da jimawa ba.

By ukarofi