Yadda yunwa ke ci gaba da kashe rayuka a gaza

Spread the love

Kungiyoyi 115 na agaji da suka haɗa da Doctors Without Borders, Saɓe the Children, Mercy Corps da Oɗfam, sun yi gargaɗi a ranar Laraba cewa, yunwar da ke addabar Gaza ta fi zama bala’i kuma “cin zarafin ɗan adam” da duniya ke kallo ba tare da yin wani abu ba.

A wata sanarwa da suka fitar tare, ƙungiyoyin sun buƙaci:

Tsagaita wuta da gaggawa, buɗe dukan mashigar ƙasa, cire duk wata shinge ga kai agaji ta hanyar MDD.

Suna masu cewa: “Abokan aikinmu da mutanen da muke taimaka wa suna gushewa cikin yunwa.”

Gwamnatin Isra’ila dai ta mayar da martani, tana cewa ba ita ke da alhakin yunwar da ke Gaza ba. Kakakin gwamnatin, Daɓid Mencer, ya ce: “Yunwar da ke Gaza ba ta hannunmu take ba. Hamas ce ta ƙirƙire ta.”

Ya ƙara da cewa, Hamas na hana kayan agaji shiga, tana ƙwace su da kanta ko amfani da su don sojoji. Sai dai bayanai daga WHO da EU sun nuna cewa Isra’ila ce ke rufe mashigar kayan agaji tun daga watan Maris, sannan ta buɗe su da matuƙar ƙuntatawa a watan Mayu.

ƙasashen Tarayyar Turai da suka haɗa da Faransa, Ireland, Spain da Netherlands sun yi tir da yadda Isra’ila ke jinkirta kayan agaji shiga Gaza. A wani taro a Brussels, wasu jakadun EU sun ce Isra’ila ba ta cika alƙawarin da ta ɗauka na yawan kayan da za su shiga Gaza.

A cewarsu, kafin rufewar mashigar agaji, motoci 500-600 na abinci da magunguna ke shiga Gaza kullum, amma yanzu ba a samun ko rabin wannan.

“Wannan yunwa ta gangan ce,” inji WHO.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana cewa: “Kashi mai yawa na jama’ar Gaza suna da yunwa. Idan ba za mu kira hakan da sunan ‘yunwa da aka shirya ba, to me za mu ce?”

Majalisar ɗinkin Duniya kuma ta ce sojojin Isra’ila sun harbe ɗaruruwan Falasɗinawa da ke ƙoƙarin karɓar abinci a wuraren rabon agaji tun daga watan Mayu.

ƙasar Brazil ta bayyana aniyarta ta shiga cikin ƙarar da Afrika ta Kudu ta shigar a gaban Kotun Duniya (ICJ) kan tuhumar Isra’ila da aikata kisan ƙare dangi a Gaza.

Shugaban majalisar ministocin Ireland, Simon Harris, ya ce: “Yunwar da ke addabar Gaza ita ce mafi muni da wannan ƙarni ya gani. Yara na mutuwa a gabanmu. Wannan babban abin kunya ne ga ɗan adam.”

By ukarofi