Daga BELLO A. BABAJI
A ƙoƙarinsa na kula da tsaftar muhalli da samar da yanayi mai kyau ga harkokin noma a jiharsa, Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya ƙaddamar da raba motoci da wasu kayayyakin aiki ga shirin tsaftace muhalli na matasa.
A ranar Talata ne gwamnan ya aiwatar da hakan a gidan gwamnatin jihar dake Gusau.
A wata sanarwa da Kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa cikin ababen hawa da aka raba sun haɗa da motocin zubar da shara guda 10 da na shara guda huɗu da manya na shara guda biyu da kuma babura 65.
Ya kuma ce shirin kula da yanayin noma na Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACReSAL) ya bada kwandunan zubar da shara na filastik guda 450 ga ofis-ofis na al’umma da wasu na ƙarfe guda 55 ga birane.
A lokacin da ya ke jawabi, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa waje mai tsafta yana taimakawa wajen janyo ra’ayoyin masu zuba hannun-jari da yawon buɗe ido da kuma samar da hanyoyin inganta al’umma.
Ya ce wannan ɗaya ne daga cikin nasarori da suka samun a tsawon watanni 20 don ceto jihar daga matsanancin halin da ta samu kanta, ya na mai bayyana kula da muhalli a matsayin ɗaya daga cikin abinda zai taimaka wa cimma manufofinsu.
Ya ƙara da cewa, hakan wani fage ne da zai bai wa matasan damar samun ayyukan yi da faɗaɗa harkokin sana’o’insu ta fuskar ƙwarewa.
Gwamna Lawal ya kuma ce a yayin da suke ƙoƙarin samar da ababen more rayuwa ga al’ummar jihar, ya na da muhimmanci a samu tsaftataccen muhalli da suka haɗa da unguwanni, kasuwanni da kuma sauran wuraren da jama’a ke gudanar da wasu harkoki, ya na mai kira ga dukkanin masu-ruwa-da-tsaki da su bada haɗin-kai wajen tabbatar da tsafta a jihar.