‘Yan bindiga sun kai hari kasuwar Monday Market a Yobe

Daga USMAN KAROFI

‘Yan bindiga sun afka kasuwar Ngalda Monday Market da ke ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe da daren Litinin, inda suka kai hari suka kashe mutane da dama tare da raunata wasu da yawa.

Shaidu sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun shiga kasuwar ne suna harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, wanda ya sa mutane suka ruga neman mafaka.

Daga nan, maharan suka nufi wuraren POS da shaguna suna kwasar kuɗaɗe masu yawa da kayayyaki masu daraja.

Rahotanni daga garin Ngalda sun tabbatar da cewa an kashe wani Alhaji Ya’u mai provision a harin, duk da cewa adadin waɗanda suka mutu ba a samu tabbaci ba.

Kasuwar Ngalda Monday Market tana ɗaya daga cikin manyan kasuwanni da ke jihar Yobe, wacce ke jawo ‘yan kasuwa da abokan ciniki daga sassan Arewa maso Gabashin Najeriya.

Har yanzu jama’ar gari na cikin firgici, inda suke kira ga hukumomi da su ƙara tsaurara matakan tsaro don kare kasuwar da unguwannin da ke kusa da ita.

Cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sanda ta Jihar Yobe ta fitar a ranar Talata, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa an kama mutum ɗaya tare da ƙwato bindiga guda ɗaya da aka ƙera a gida.