Tinubu, Fubara, Wike da jagororin Ogoni sun shiga ganawar sirri

Daga USMAN KAROFI

A ranar Talata, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu tare da Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, sun gudanar da ganawar sirri da wata tawagar shugabannin Ogoni ƙarƙashin jagorancin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas. Taron, wanda ya samu halartar manyan jami’an gwamnati ciki har da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila; mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu; babban jami’in zartarwa na kamfanin mai na ƙasa (NNPCL), Mele Kyari; ministan yaɗa labarai , Mohammed Idris; da wasu ministoci da hadimai, ya gudana ne a lokacin da rikici ke ci gaba tsakanin Wike da Fubara. Wannan rikici ya samo asali daga rashin jituwa tsakanin tsohon gwamnan jihar Ribas, Wike, da magajinsa, Fubara, duk da kasancewarsu abokan siyasa a baya.

Taron ya biyo bayan kiran wata ƙungiyar ƙungiyoyin farar hula da suka nemi gwamnatin tarayya ta ware dala tiriliyan ɗaya ($1 trillion) domin share yankin Neja Delta da biyan diyya ga mutanen da suka rasa rayukansu saboda gurɓacewar muhalli da lalacewar rayuwar al’umma sakamakon ayyukan hako mai a Ogoniland.

Ƙungiyar ta haɗa kungiyoyi irin su “Environmental Rights Action/Friends of the Earth Nigeria” “Corporate Accountability and Public Participation Africa” da “Health of Mother Earth Foundation”, waɗanda suka jaddada buƙatar gwamnati ta daina shirye-shiryen farfaɗo da hako mai a yankin har sai an magance matsalolin muhalli. Sun kuma soki wannan shiri na gwamnati, suna mai bayyana shi a matsayin rashin adalcin muhalli, tare da jaddada rahoton UNEP na shekarar 2011 wanda ya nuna yadda ayyukan haƙo mai suka haifar da gagarumar lalacewar muhalli a Ogoniland.

Shugaban hukumar cigaban Niger Delta (NDDC), Samuel Ogbuku, ya nuna damuwa kan yadda rikice-rikice da ke addabar yankin suka jawo kamfanonin mai na duniya suka dakatar da ayyukansu a Ogoniland. Ya ce wannan matsala ta haifar da babbar koma baya ga tattalin arzikin ƙasa, musamman ma a wannan lokaci da ake fama da karin matsalar makamashi bayan cire tallafin mai daga gwamnatin tarayya.

Gwamnati, a nata ɓangaren, ta nuna damuwa kan doguwar dakatarwar hako mai a jihar Ribas, tana mai bayyana shirin share yankin Ogoni a matsayin matakin gyara wanda zai ba da dama ga farfadowar harkar haƙo mai a yankin. Duk da haka, al’ummomin yankin sun dage cewa sai an ɗauki matakan gyara muhalli da biyan diyya kafin a ci gaba da haƙo mai.