Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da bai wa mata kimanin 2383 wanda tace za su amfana da tallafin awaki kimanin 7,158 dan su zama masu dogaro da Kan su da bunƙasar tattalin arziki.
Gwamna Abba Kabir na Jihar Kano ya shaida haka yayin da ya ƙaddamar da fara bada tallafin dabbobin a anguwar Mariri da ke Ƙaramar hukumar Kumbotso da ke Jihar Kano Karo na biyu a zuwan gwamnatin shi.
Haka kuma ya Ƙara da cewa bayan baiwa matan wannan adadin dabbobin gwamnatin shi za ta ƙara ba matasa su 671 shanu kimanin 1342 sai raguna 1822 ga mutane 911 dan tabbatar da an samu dukkan hanyar dogaro da kai.
“Wannan yana ɗaya daga cikin alƙawura da muka ɗaukar ma ku na cewar zamu nemo dukkan hanyar da ta dace dan Ƙara maku jarin da zai taimaka maku wajen riƙe gidajen ku da kula da harkokin yau da kullum.
“Kamar yadda muka san ku da kula wajen riƙe Ƙaramar sana’a ta kai wani matakin nasara a rayuwar ku muna horan ku da ku riƙe wannan dabbobin tare da kiwata su in ji shi.”
Gwamnan ya kuma cewa shine Karo na biyu da wannan gwamnati ta rabawa mata daga Ƙananan hukumomi 44 dake faɗin Jihar Kano irin wannan tallafi da zai zama hanyar dogaro dakai gare du.
“Ɓangaren awaki zamu ba kowace mace Akuya ɗaya da Ƙananan awaki biyu,sai ɓangaren natasa kuma utum 671 za su amfana da tallafin shanu 1342 yayin da za su rabawa mutane 911 raguna 1822 domin kiwatawa tare da samun hanyar dogaro da kai.
Alhaji Abba Kabir ya kuma gargaɗi waɗanda za su amfana da tallafin dan zama da ƙafafun su domin da taimkon kaucema fadawa mugun yanayin rayuwa da yaƙar talauci da rashin aikin yi.
Gwamnan ya kuma yaba da irin yadda bankin musulunci ya ke ƙara taimakawa wajen ganin an yaki talauci a Jihar Kano musamman ma’aikatar Kula da harkokin noma tare da hukumar KNARDA da Sauran masu ruwa da tsaki.
A wani Labarin kuma gwamnan ya baiwa wata baiwar Allah mai suna Hassana Nazifi yar asalin Ƙaramar hukumar Minjibir aiki nan take tare da sanya ta cikin kwamitin da zai ƙaddamar na Kula da masu buƙata ta musamman a Jihar Kano.
Gwamnan ya kuma yaba da irin wannan kwamitin da ya zabo waɗanda za’a baiwa wannan tallafi ciki harda wannan baiwar Allah Malama Hassana daga Karamar hukumar Minjibir da a yau ya bayyana kudurin shi na bats wannan mukami dan inganta harkokin masu buƙata ta musamman.