Gwamnati ta fitar da hotuna da sunayen waɗanda su ka tsere daga gidan yarin Suleja

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukumar gyaran hali ta ƙasa (NCoS), ta fitar da hotuna da sunaye da sauran bayanan waɗansu mutane da su ka tsere daga kurkukun Suleja, reshen Abuja, sakamakon ruftawar ginin da su ke ciki bayan wani mamakon ruwan sama da aka yi a ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu, 2024.

Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abubakar Umar ya fitar a ranar Alhamis, ta ce matakin yana da muhimmanci wajen sake kamo su tare da mayar da su komar hukumar.

Ya ce, sun miƙa bayanan waɗanda suka tseren ga sauran hukumomin tsaro da kuma al’umma, a yunƙurinsu na gano waɗanda su ka tseren inda su ka buƙaci mutane su bada haɗin kai wajen kamo su kasancewar su haɗari a cikin al’umma.

Umar ya ƙara da cewa, idan aka ga wani daga cikin su, to a sanar da hukuma mafi kusa, ko kuma a kira ɗaya daga cikin lambobi kamar haka: 07087086005, 09060004598 da 08075050006 ko kuma ta adireshi kamar haka: [email protected] ko kuma [email protected].

By Babaji