Gwamnatin Tarayya za ta ƙirƙiri kotunan tafi-da-gidanka don yaƙar cin zarafi

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya za ta kafa kotunan tafi-da-gidanka don magance matsalolin da suka shafi fyaɗe da sauran cin zarafi cikin gida.

Ministar Harkokin Mata, Uju Kennedy-Ohanenye ce ta sanar da hakan a yayin wani taron kwana guda na masu ruwa da tsaki na kasa kan magance cin zarafi, da aka gudanar ranar Talata a Abuja.

Hukumar ICPC tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Magance Matsalar Cin Zarafi ne suka shirya taron.

Kennedy-Ohanenye ta bayyana damuwarta kan yadda ake samun yawaitar cin zarafi musamman a manyan makarantun ƙasar nan, ta kuma jaddada cewa ana aiwatar da sabbin matakai na magance wannan matsala.

“Tsarin cin zarafi ya ta’allaƙa ga manyan makarantu; Haka kuma yana faruwa a makarantun firamare da sakandare, wanda malamai ke aikatawa a wasu lokutan kuma a tsakanin ɗalibai,” inji ta.

“Mu na kuma haɗa kai da masu otel don hana yara masu ƙarancin shekaru masauki da kuma kai rahoto ga jami’an tsaro don daƙile wannan matsala.”

Ta buƙaci masu ruwa da tsaki da su magance cin zarafi da ƙarfi don rage kyama da rashin kima a tsakanin waɗanda abin ya shafa.

Dr. Musa Aliyu, Shugaban Hukumar ICPC kuma Babban Lauyan Nijeriya (SAN), ya bayyana buƙatar aiwatar da mugun sakamako ga masu aikata laifuka domin daƙile yawaitar cin zarafin mata.

Ya yi nuni da cewa cin zarafi da sauran matsalolin al’umma da suka haɗa da nuna banbancin jinsi suna ɓata sunan al’umma.

“Sai dai daidaitaccen yaƙin, mai dagewa, mai da hankali, da haɗin kai zai iya magance ƙalubalen cin zarafin mata a manyan makarantu,” inji Aliyu.

“A ‘yan shekarun da suka gabata, ICPC, tare da goyon bayan gidauniyar Ford, ta aiwatar da wani aiki da nufin magance wannan batu na al’umma, wanda ya haifar da tsara tsarin cin zarafin mata ga cibiyoyin ilimi.”

Ya bayyana cewa, hukumar ta hada hannu da ‘Gender Mobile Initiatiɓe’ don tsara wani tsari na koyi ga manyan makarantun, wanda ma’aikatar ilimi ta tarayya ta amince da na makarantun firamare da manyan makarantu.

“Waɗannan manufofin ba lallai ba ne a yi nufin masu ruwa da tsaki su amince da su baki ɗaya,” inji Aliyu. “Ya kamata su zama jagororin abin da cikakkiyar manufa ta ƙunshi, kuma kowace cibiyar da ke son yin hakan za ta iya karɓe su gaba ɗaya.”

Ya tunatar da mahalarta cewa kowa, ba tare da la’akari da matsayi, matsayi, ko jinsi ba, na iya zama wanda aka azabtar ko mai yin lalata.

“Nijeriya tana da dokoki da manufofi da yawa, amma da yawa ba a aiwatar da su daidai ba,” inji shi. “Tsarin aiwatar da manufofin samfurin yana da muhimmanci. Nasarar wannan shiri ya ta’allaka ne kan yadda masu ruwa da tsaki suka taka rawar gani da kuma jajircewarsu.”

Omowumi Ogunrotimi, wanda ya kafa kuma Babban Darakta na Tsarin Wayar da Kai kan Cin Zarafi ya buƙaci masu ruwa da tsaki su mai da hankali kan rigakafin maimakon tsarin mayar da martani. “Wannan shi ne dalilin da ya sa muke haɗa kai da ICPC don tabbatar da manufar da muka tsara tare ya samo asali ne na hada-hadar jama’a,” inji ta.

Ta tuna cewa a 2019 da 2020, an gudanar da taron ƙasa don tabbatar da wannan manufa tare da masu ruwa da tsaki, ciki har da Hukumar Kula da Jami’o’i ta ƙasa (NUC), Hukumar Kula da Ilimin Fasaha ta ƙasa (NBTE), da kuma ƙungiyar ɗalibai.

Ogunrotimi ya ƙara da cewa, “Manufofin sun shafi jagoranci, shiga, buri, da kuma gogewar waɗanda rashin adalcin tsarin ya shafa, musamman al’ummar dalibai,” inji Ogunrotimi. “Muna da burin ciyar da wannan gaba ne saboda a Nijeriya, manufofin ba sa fassara kai tsaye zuwa aiwatarwa.

Don haka ne mu ka jawo mahalarta daga sassan ƙasar nan, ciki har da kwamishinonin ilimi na jihohi sama da 25, domin su shiga tsarin wannan shirin.”

By ukarofi