

Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da sayar da tan 30,000 na shinkafa akan farashin kuɗi Naira 40,000 babban buhu domin rage matsalar hauhawar farashin abinci a Najeriya.
Shirin, wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta na da nufin samar da abinci mai sauƙi ga ƴan ƙasa.
Za a sayar da shinkafar kan karyayyen farashin a duk faɗin ƙasar ƙarƙashin tsauraran matakan da za su tabbatar da an bi dokokin da suka dace wajen hana Shinkafar shiga hannayen ƴan kasuwa masu tsauwala farashi da gangan.
