Akwai buƙatar ƙarfafa haɗin-gwiwa tsakanin sarakuna da gwamnati wajen daƙile matsalolin ƙasa – Shettima

Spread the love

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya yi kira da a ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin gwamnatin tarayya da Masarautun gargajiya.

Shettima ya yaba da rawar da suke takawa wajen wanzar da haɗin-kan ƙasa da zaman lafiyar al’umma.

Mataimakin ya bayyana hakan ne a wajen ta’aziyyar da ya kai masarautar Ningi da ke jihar Bauchi, bisa rasuwar marigayi Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Ɗanyaya.

Ya kuma taya sabon sarkin da aka naɗa murna tare da yi masa alƙawarin ba shi goyon bayan gwamnatin tarayya.

Ya ƙara da jaddada muhimmancin cigaba da shugabancin sarakunan gargajiya ga haɗin-kan ƙasa.

By Babaji