Tsadar man fetur ya tsananta ayyukanmu – Ƙungiyar Masana’antu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaban Ƙungiyar Masana’antu ta Nijeriya (MAN) reshen Kudu-maso-Yamma, Mista Lanre Popoola ya ce ayyukan masana’antu sun tsananta sakamakon ƙarin kuɗin man fetur da aka yi kwanan nan.

Ya faɗi hakan ne a yayin zantawa da jaridar ‘News Agency Nigeria’ a Ibadan, babban birnin jihar Oyo inda ya bayyana yadda tsananin da aka shiga a matsayin dalili na rashin gudanar da ayyukan masana’antun yadda aka saba sakamakon koma baya da hakan ya haifar.

Ya ce, tun kafin ƙarin farashin man fetur a Nijeriya, MAN ke fuskantar tsanani wajen amsa buƙatun kwastomominsu.

Ya kuma ce, a halin tsaka-mai-wuya da tattalin arziƙin ƙasa ke ciki kuma Gwamnatin Tarayya ke son masana’antun ƴan kasuwa su ƙaddamar da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 da aka yarje a ƙasar.

Ya ƙara da cewa, ɓangaren na fuskantar matsin tattali na hauhawar farashi da rugujewar Naira wanda hakan ya sanya suka shiga halin da suka tsinci kansu.

A kwanakin baya ne Kamfanin Man fetur na Ƙasa, NNPCL ya yi kwaskwarima wa farashin litar mai inda ya mayar da shi daga N580 zuwa N855 da N1,200 la’akari da wajen da ake saya.

By Babaji