Gwamnati ta rusa gidajen masu garkuwa da mutane a Binuwai

Daga WAKILINMU

Bayanai daga Jihar Binuwai sun nuna gwamnatin jihar ta rusa wasu gidaje guda biyu waɗanda ake zargin mallakar wani mai harkar satar mutane ne mai suna Aondofa Cephas Chekele wanda aka fi sani da Azonto.

A ranar Litinin da ta gabata gwamnatin jihar ta ɗauki matakin rusa gidajen domin ya zama gargaɗi ga waɗanda ke hana zaman lafiya zama da gidinta a jihar.

Binciken Manhaja ya gano cewa Azonto shi ne mataimakin gawurtacen ɗan bindigar nan da aka kashe a jihar a Satumban 2020, wato Terwase Akwaza da aka fi sani da Gana.

‘Yan sanda ne suka jagoranci rusa gidajen a Makurɗi, wanda aka aiwatar ƙarƙashin dokar yaƙi da harkokin garkuwa da mutane ta 2017 wadda Gwamna Samuel Ortom ya sanya wa hannu a wancan lokaci.