NNPC ya bayyana dalilinsa na neman sayen kaso a matatar man Ɗangote

Daga UMAR M. GOMBE

Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) ya bayyana dalilin da ya sa yake neman sayen wani kaso a matatar mai na Ɗangote.

NNPC ya bayyana hakan ne ta bakin shugabansa Mele Kyari, yayin wani shirin talabijin da aka yi da shi a tashar ChannelsTV a ranar Talata.

Ya zuwa 2022 ake sa ran matatar Ɗangote ta soma aiki inda za ta riƙa tace mai har ganga 650,000 a kowace rana. Lamarin da ake kallo da muhimmiyar cigaba a fannin makamashi a Nijeriya da ma Afirka baki ɗaya.

Tun a Mayun da ya gabata NNPC ya bayyana cewa yana shirin mallakar kashi 20 na hannun jarin matatar mai mai zaman kanta wadda kamfanin Aliko Ɗangote zai buɗe.


Da yake bayani yayin shirin, Kyari ya ce “Babu wata ƙasa da ta dogara da albarkatu da za ta ci gaba da zura ido a harkar kasuwanci mai ƙarfi irin wannan da ke da tasiri a sha’anin tattalin arzikin ƙasa, kuma a ce wai ƙasar ba ta da wani abin faɗa a ciki.”

Yana mai cewa sanin irin riba mai tsoka da ke tattare da harkar masana’antar matatar mai ya sanya NNPC yanke shawarar zuba jarinsa.

Ya ci gaba da cewa, “Jarin da za a zuba a matatar mai ta Ɗangote, ba wai kuɗin gwamnati za mu ɗauka mu yi amfani da shi ba, rance za mu kinkimo domin mu shiga a yi da mu.

“Muna sane da cewa harkar matatar mai abu ne mai riba da amfani, za ta bayar da gudummawa mai ɗorewa ga tattalin arziki.”

Ya ce “Wannan ne dalilin da ya sa bankuna suke ba mu rance, don haka za mu iya sayan hannun jari a ciki.”