Yadda bikin komawar Matawalle APC ya kasance

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

A wannan Talatar Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle ya sauya sheƙa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya koma All Progressive Congress (APC) jam’iyya mai mulki a ƙasar nan.

Da yake jawabi a yayin bikin sauya shelarsa zuwa APC, da aka gudanar a katafariyar kasuwar baje koli ta Zamfara da ke Gusau, Matawalle ya ce yanzu shi ne shugaban APC a Zamfara.

Matawalle ya yi kira ga dukkan mambobi da magoya bayan APC a jihar da su haɗa kai su gina sabuwar Zamfara da APC gabanin babban zaɓen 2023.

Matawalle ya yaba wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, shugabannin kwamitin riƙo na ƙasa na jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin Alhaji Maimala Buni, tsohon Gwamna Abdulaziz Yari haɗa da masu ruwa da tsaki bisa fahimtar su, tare da yin alƙawarin tafiya da kowa da kowa bai ɗaya don cigaban APC da jihar Zamfara baki ɗaya .

A cewarsa, “Daga yau, na zama shugaban jam’iyyar APC a Zamfara kuma dukkan shugabannin jam’iyyar APC an rusa su, kuma za mu yi aiki ba tare da gajiyawa ba don tabbatar da haɗin kai da cigaban APC a jihar ta Zamfara da kuma matakin ƙasa.”

A nasa jawabin, shugaban kwamitin riƙo na jam’iyyar APC, Alhaji Maimala Buni, ya nuna farin cikinsa game da sauya sheƙar da Gwamna Matawalle ya yi zuwa APC a jihar Zamfara, yana mai jaddada cewa shugabannin jam’iyyar APC na ƙasa za su haɗa kai da Gwamna Bello Mohammed Matawalle don cimma burin da ake so.

Manhaja ta ruwaito cewa, Gwamnonin Kano, Neja, Kaduna, Katsina, Borno, Kebbi, Platue, Gombe, Kogi da wakilan Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, Ali Modu Sheriff, Sanata Ahmed Sani Yerima da sauran manyan baki sun kasance cikin wadanda suka halarci taron.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, dukkan sanatocin uku, mambobin majalisar wakilai shida, mambobin majalisar dokokin jihar Zamfara 26 su ma sun bi Gwamna Bello Mohammed Matawalle zuwa APC, ban da mataimakin Gwamna Mahadi Aliyu Gusau wanda ya ƙi bin shi.