Raina kotu ya janyo wa Jacob Zuma zaman gidan yari na watanni 15

Babbar kotun ƙasar Afirka ta Kudu ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar Jacob Zuma hukuncin zaman gidan yari na watanni 15, bayan samunsa da aikata laifin raina kotu, biyo bayan ƙin bayyana a gaban masu binciken zargin rashawa da aka yi masa.

An shaida wa Zuma cewa ya miƙa kansa nan da kwanaki 5, kuma idan ya ƙi yin biyayya za a umurci ‘yan sanda su tisa ƙeyarsa zuwa kurkuku.

Wannan hukunci abu ne da ba a saba gani ba kuma cike yake da tarihi, don kuwa ya zama abin misali ga Afirka ta Kudu da ma nahiyar Afirka baki ɗaya, ta fuskar jefa tsohon shugaba a kurkuku saboda ƙin bada haɗin kai ga binciken rashawa.

Yayin yanke hukuncin, Alƙali Sisi Khampepe ta ce an samu Jacob Zuma da laifin raina kotu, alhali ba wanda ya fi ƙarfin doka.

Ana zargin Zuma mai shekaru 79 da samar da yanayi da ya bada damar wawushe dukiyar al’umma kusan shekaru 9 da ya shafe yana mulkin ƙasar kafin jam’iyyar ANC ta ƙwace mulki a 2018.